PRINCIPLES OF GRAPHIC DESIGN
1. Balance (Daidaito)
Ma’ana: Daidaito yana nufin yadda abubuwa ke rarrabuwa cikin zane don kada bangare guda ya fi wani nauyi ko jawo hankali. Wannan yana nufin rarraba abubuwa a cikin zane ta yadda zai bayar da jin daɗin kwanciyar hankali ko daidaituwa.
TYPES OF BALANCE
Symmetrical Balance (Daidaito Mai Tsari): Shine abubuwan da suke kama da juna dama da hagu.
Asymmetric Balance (Daidaito Mara Tsari): Wannan ana raba abubuwa ta hanyoyi daban - daban amma suna daidai da juna.
Radial Balance (Daidaito Mai Zagaye): Wannan abubuwan suna zagaye da wata cibiyar tsakiya, kamar Rana da hasken ta.
2. Contrast (Bambanci)
Ma’ana: Bambanci yana nufin amfani da abubuwa masu sabanin juna (irin su launi, girma, ko siffa) don jawo hankali ko jaddada sako. Wannan shine amfani da abubuwan zane-zane da suke da bambanci sosai da juna don jawo hankali da samar da sha'awa. Misali, babban rubutu da ƙarami, launi mai haske da mai duhu, siffa mai santsi da mai kaushi. Contrast yana taimakawa wajen sa abubuwa su fita fili kuma su zama masu sauƙin gani.
3. Emphasis ( Bayyanawa ko Jaddadawa)
Ma’ana: Emphasis na nufin jaddada wani abu a cikin zane don ya ja hankali fiye da sauran abubuwa. Wannan yana nufin ba da fifiko ga wani abu ko wani sashi na zane don jawo hankalin mai kallo a wurin farko. Ana iya yin wannan ta amfani da girma, launi, sabani, ko kuma sanya abu a wuri na musamman. Manufar ita ce a tabbatar cewa mai kallo ya lura da saƙo ko abu mafi mahimmanci.
4. Movement (Tafiya ko Gudu )
Ma’ana: Movement yana nufin yadda idon mutum ke bi ko yawo a cikin zane. Wannan yana nufin yadda idon mai kallo ke zagaya a cikin zane. Mai zane yana jagorantar idon mai kallo ta amfani da layuka, sifofi, launuka, da tsarin abubuwa. Yana taimakawa wajen faɗar labari ko kuma nuna jeri na mahimmanci.
5. Proportion (Daidaiton Girma)
Ma’ana: Proportion yana nufin alaƙar girman abubuwa da juna a cikin zane. Yana nuna muhimmanci ko kusanci tsakanin abubuwa.Wannan yana nufin yadda girman abubuwa daban-daban a cikin zane suke da alaƙa da juna da kuma ga dukan zane. Idan abubuwa suna da daidaitaccen girma, zane yana da kyau kuma yana da ma'ana. Idan babu daidaitaccen girma, zane na iya zama abin kunar rai ko kuma mara ma'ana.
6. Rhythm ( Yanayi Mai Maimaituwa)
Ma’ana: Rhythm a zane yana nufin amfani da abubuwa masu maimaituwa (kamar siffofi, launuka, ko layi) don ƙirƙirar nutsuwa ko motsi. Wannan yana nufin maimaita abubuwa ko siffofi a cikin zane wanda ke haifar da jin motsi ko kuma tsari mai daɗi.
TYPES OF RHYTHM
Regular Rhythm (Rhythm Mai Tsari): Wannan abubuwan suna maimaituwa daidai da juna.
Irregular Rhythm (Rhythm Mara Tsari): Wannan abubuwa suna maimaituwa amma ba da cikakken tsari ba.
Progressive Rhythm (Rhythm Mai Ƙara Ƙarfi): Wannan abubuwan suna girma ko raguwa a hankali don samar da motsi.
7. Alignment ( Tsari ko Tsayuwa Cikin Layi)
Ma’ana: Alignment yana tabbatar da cewa abubuwa suna da tsari da jere mai kyau. Yana kara karantawa da kyan gani. Wannan yana nufin tsara abubuwa a cikin zane ta hanyar daidaita su gefe da gefe ko sama da ƙasa. Rubutun da aka daidaita yana da sauƙin karantawa, kuma hotuna da aka daidaita suna ba da jin daɗin gani.
8. Repetition (Maimaitawa)
Ma’ana: Repetition na nufin amfani da abu guda sau da dama a cikin zane don ƙarfafa shaida ko tsarin gani. Wannan shine maimaita wani abu ko wani sifa a cikin zane. Maimaitawa yana taimakawa wajen ƙirƙirar haɗin kai, jituwa, da kuma ƙarfafa wani saƙo. Misali, maimaita launi ɗaya ko siffa ɗaya a wurare daban-daban na iya sa zane ya zama mai haɗin kai.
9. Proximity ( Kusanci ko Ƙulla Wuri)
Ma’ana: Proximity yana nufin sanya abubuwa masu alaƙa da juna a wuri ɗaya ko kusa, domin su zama ƙungiya ɗaya a idon mai gani. Wannan yana nufin sanya abubuwa masu alaƙa kusa da juna. Idan abubuwa biyu suna kusa da juna, idon mai kallo yana ganin su a matsayin wani abu ɗaya ko kuma suna da alaƙa. Wannan yana taimakawa wajen tsara bayanai da kuma sa zane ya zama mai sauƙin fahimta.
10. Pattern (Tsari Mai Ma’ana ko Jere)
Ma’ana: Pattern yana nufin ƙirƙirar tsarin da ke maimaituwa – kamar ado ko ƙirar bango. Ana amfani da shi don kawata ko jaddada yanayi. Tsari shine maimaita abubuwan zane-zane a cikin wata hanya mai tsari ko wani jeri mai maimaitawa. Wannan na iya zama tsarin layuka, siffofi, ko launuka.
TYPES OF PATTERN
Geometric Pattern: Wannan suna amfani da siffofi masu tsari kamar circle, square, triangle da sauran su .
Organic Pattern: Wannan sun dogara ne da siffofi na halitta kamar ganye, furanni ko igiyar ruwa da sauran su.
Abstract Pattern: Wannan na nufin maimaita abubuwa ba tare da tsari na yau da kullum ba.
11. Variety ( Bambance-bambance)
Ma’ana: Variety yana nufin amfani da abubuwa daban-daban kamar launi, siffa, font, da dai sauransu. Wannan yana nufin abubuwa daban - daban domin ya kasance mai ban sha'awa kuma kada ya zama mai ɗaukar ido. Idan zane yayi kama da juna gaba ɗaya, yana iya zama mai gundumar. A iya samar da banbanci kamar haka light da dark, big da small, bold da thin da sauran su.
12. Hierarchy ( Matsayi ko Mataki)
Ma’ana: Hierarchy yana nuna abubuwan da suka fi muhimmanci da kuma hanyoyin da za su fara jawo hankali. Wannan yana nufin tsara abubuwa a cikin zane ta yadda mai kallo zai fahimci wane abu ne ya fi muhimmanci. Ana iya yin wannan ta amfani da girma, launi, matsayi, ko kuma nau'in rubutu. Yana taimakawa wajen jagorantar idon mai kallo da kuma tabbatar da cewa an fahimci saƙon da kyau.













0 Comments
Shigar da tambayar ka, shawara ko ƙarin bayani a sashen comment.