GABATARWAR ZANE - INTRODUCTION TO GRAPHIC DESIGN
Zane-zanen hoto (Graphic Design) wata hanya ce ta sadarwa da ake amfani da hoto, launi, rubutu, da siffofi don isar da saƙo ga masu kallo. Manufarsa ita ce yin tasiri, jan hankali, ko bayyana wani bayani ta hanyar gani (visual). Ana iya amfani da zane-zanen hoto a fannoni daban-daban.
Graphic design wata fasahace da ake amfani da ita wajen haɗa rubutu, launuka da hotuna don ƙirƙirar kayayyakin gani na musamman na sadarwa. Wannan fasaha tana taka muhimmiyar rawa wajan bayyana sakonni da kuma burge masu kallo. A yau graphic design na da amfani daban-daban kamar kasuwanci, talla, bidiyo, wallafa da sauransu.
Manufar graphic design ita ce haɗa dabarun zane da ilimin sadarwa don ƙirƙirar abubuwan gani waɗanda zasu ja hankalin mutane, Sukuma isar da saƙon da aka nufa cikin sauƙi. Misalan abubuwan da graphic designer ke ƙirƙirawa sun hada da tambura (logos) tallace – tallacen mujallu, hotunan internet da sauran kayayyakin aiki na gani.
A yau, zane-zanen hoto ya zama ɗaya daga cikin manyan hanyoyin sadarwa a duniya. Yana taimakawa wajen: Faɗakarwa da ilmantarwa: Kamar yadda ake amfani da infographics ko zane don bayani a asibiti ko makaranta. Tallata kaya ko sabis: Kamfanoni suna amfani da zane don jawo hankalin mutane su sayi kayayyakinsu. Gina alamar kamfani: Logo da launuka na musamman suna sa mutane su gane kamfani cikin sauki. Inganta kwarewa ta masu amfani: Musamman a UI/UX (wato fuskar app ko website), don sauƙaƙa amfani da kayayyaki ko ayyuka.
DEFINITION OF GRAPHIC DESIGN
Graphic design wata hanya ce da ake ƙirƙirar kayayyakin gani da ake amfani da su wajen sadarwa. Wannan fasaha ta haɗa da harufa, launuka, zane -zane, hotuna da tsari domin isar da saƙonni a cikin hanya mai jan hankali da fahimta.
Graphic design wata hanya ce ta sadarwar gani, Wato ta amfani da hotuna, launuka, zane y da rubutu domin isar da saƙo cikin salo mai jan hankali.
TOOLS FOR GRAPHIC DESIGN
Graphic design tools waɗan su kayayyaki ne da graphic designer ya ke amfani da su wajen ƙirƙirar abubuwan gani, Kula da su, tsara su da ma yaɗa su. Wannan tools sun kasu gida biyu, kashi na farko hardware na biyu kuma software.
HARDWARE
Computers, Smartphone, Graphic Tablet, Printer da sauran su.
SOFTWARE
Adobe Photoshop, Illustrator, Figma, Corel draw, Canva, Notion, Iconfinder, Google fonts da Adobe colour da sauran su.
IDAN MAI KARATU NA DA TAMBAYA ZAI IYA YIN COMMENT KO A GROUPS ƊIN MU NA WHATSAPP DA TELEGRAM.
WHATSAPP GROUP 👇
TELEGRAM GROUP 👇

0 Comments
Shigar da tambayar ka, shawara ko ƙarin bayani a sashen comment.