TARIHIN ZANE - HISTORY OF GRAPHIC DESIGN


ZAMANIN DA {ANCIENT TIME}

     

     A zamanin da mutane suna amfani da zanen dutse da a kafi sani da phitographs domin sadarwa. A misra ana amfani da hieroglyphs a bango don bayyanar da al’adunsu. Zanen bangon kogo a wurare kamar Lascaux (a Faransa), inda ake nuna mutane suna farauta. Zanen al’adu a tsofaffin al’ummomi kamar Masarawa, Babilawa, da Sinawa inda ake amfani da zane wajen bayani da tarihi. Wannan ya kasance farkon tsarin sadarwa na gani kafin Æ™irÆ™irar haruffa ko rubuce-rubuce.


ZAMANIN BUGAWA {PRINTING ERA-1400s}

   

    A karni na 15, buga littafai ya zama ruwan dare bayan JOHANNES GUTENBERG ya Æ™irÆ™iri injin buga littafai(Movable Printing press) a shekarar 1440. Wannan ya saukaka wallafa da rarraba littattafai da mujllu. Har ila yau, an fara amfani da dabarun zane don Æ™awata mujallu da littattafai.


ZAMANIN MASANA’ANTU {INDUSTRIAL REVOLUTION-1800s}

     

   A karni na sha takwas 18 zuwa na sha tara 19, lokacin da masana’antu suka bunÆ™asa, an asamu cigaba sosai a fannin bugawa da zane –zane. Kanfanunuwa sun fara amfani da tallace–tallace don jawo hankalin kwastomomi wannan ya haifar da buÆ™atar graphic designers. Samuwar injinan bugu da kasuwanci ya sa an fara bukatar poster, logo, da advertisement design. Kamfanoni sun fara amfani da graphic design don jan hankalin abokan ciniki.


ZAMANIN BAUHAUS {BAUHAU -1920s}

     

   A karni na 20 musamman bayan 1920s graphic design ya bunkasa sosai. fFannin ya samu tasirin al’adun zamani, musamman daga kungiyar Bauhaus, wacce ta maida da hankali kan kirkirar kayayyaki masu sauki kuma masu kayatarwa.


ZAMANIN DIGITAL {DIGITAL ERA }

     

     A yanzu da hardware kamar Computer, Smartphone daTablet da kuma software kamar Adobe-photoshop, Illusrator, Coreldraw da Canva da saransu, graphic design ya koma digital. Ayau, ana amfani da kwamfuta duk wajan Æ™irÆ™irar wani abu da graphic designer ke bukata, daga tambura zuwa kayan aiki na tallace – tallace. A yau zane ya hadu da fasahar zamani sosai ana amfani dashi a shafukan yanar gizo musamman UI/UX , tallan kayayyaki a shafukan sada zumunta, motion graphics (hoto mai motsi), Artifitial intelligence (AI).
     
   Tarihin zane ya nuna yadda wannan sana’a ta ci gaba zamanin kogo zuwa digital, wannan yana kara jaddada muhimmancinsa a rayuwa ta yau da kullun. Manufar ita ce haÉ—a fasaha da sadarwa don Æ™irÆ™irar abubuwan dake bayani don tallata abu.


IDAN MAI KARATU NA DA TAMBAYA ZAI IYA YIN COMMENT KO A GROUPS ÆŠIN MU NA WHATSAPP DA TELEGRAM.




WHATSAPP GROUP 👇


TELEGRAM GROUP 👇